
Dakarun rundunar sojan Najeriya dake aiki samar da tsaro a rundunar Operation sun kama wata mata mai suna Shamsiya Ahadu da ake zargi da kai wa ƴan fashin daji makamai a jihar Zamfara.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro a Najeriya an kama matar ne biyo bayan bayanan sirri da sojojin suka samu na ƙoƙarin safarar makamai a yankin.
Hakan ya sa dakarun su ka yi gaggawar kafa shingen binciken ababen hawa a tsakanin Kware zuwa Badarawa dake ƙaramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara abin da ya kai ga an kama matar ɗauke da tarin harsashi.
A lokacin da aka kamata matar na ɗauke da harsashi 764 gidan zuba harsashi guda 6 da kuma wasu layu.
Har ila yau sojojin sun tsare wani mai suna Ahmed Hussaini wanda shi ne mai babur ɗin da yake dauke da matar