
Dorcas Omotosho wata dalibar makarantar kimiyya da fasaha ta jihar Kogi ta rasa ranta a lokacin da ta yi kokarin zubar da cikin da take da shi ɗan wata shida.
Lamarin marar dadi dake da tayar da hankali ya faru ne a ranar Talata 26 ga watan Agusta a wani asibiti mai zaman kansa dake ake kira da Al-Hassan Clinic & Maternity dake unguwar Sarkin Noma a Lokoja babban birnin jihar.
Binciken da jaridar Guardian ta gudanar ya gano cewa marigayiyar ta nemi asibitin ya zubar mata da cikin da take da shi mai wata shida. An samu nasarar zubar da cikin amma likitocin sun gaza tsayar da jinin da yake zuba inda hakan ya yi sanadiyar ajalinta.
Bayan mutuwar ta ce aka sanar da jami’an tsaro inda suka gudanar da bincike kafin daga bisani su dauke gawar ya zuwa dakin ajiye gawarwaki na Asibitin Koyarwa na Tarayya dake Lokoja.
Har ila yau jami’an yan sanda sun tsare mamallakin asibitin a sashen binciken manyan laifuka na rundunar yan sandan jihar.