Da alamun dai da sauran rina a kaba game da tsarin da za’a bi wajen zaben fidda gwani na ‘yan takarar kujerar gwamna a inuwar jam’iyar APC dake mulki,musamman a jihohin Adamawa da Taraba,inda shugabanin jam’iyar na kasa ke tabbatar da cewa ra’ayi mafi rinjaye ne za’a bi domin fidda dan takara walau ta hanyar amfani da wakilai wanda aka fi sani da delegates ko kuma yar tinke.
Kwamred Mustapha Salisu dake zama mataimakin shugaban jam’iyar ta APC a Najeriya mai kula da jihohin Arewa maso Gabas, yace sun sami korafe korafe da dama a jihohin Adamawa da Taraba to amma za’a bi ra’ayin dake da rinjaye ne na ‘yan kwamitin jihohi.
Wannan ma kuma na zuwa ne yayin da ‘yan takara irinsu Mallam Nuhu Ribadu,tsohon shugaban hukumar EFCC,ke cewa wannan karon dole a samu sauyi .