Wasu mutane biyu masu garkuwa da mutane sun shiga hannun ƴan sanda a jihar Filato

Rundunar Ƴan sandan jihar Filato ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zarginsu da yin garkuwa da wani mutum mai suna, Nijin John ranar Juma’ar da ta wuce a Rankiya dake ƙaramar hukumar Jos South.

Jami’an ƴan sandan sun samu nasarar ceto mutumin da aka sace ne biyo bayan wata musayar wuta da suka yi da masu garkuwar inda suka gudu suka barshi a cikin daji.

Da yake nunawa manema labarai mutanen a ofishin ƴan sanda dake Rantiya mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, DSP Alabo Alfred ya ce an kama mutanen ne lokacin da suke tserewa sakamakon ƙoƙarin DPO na Rantiya da kuma mutanensa.

Ya ce an kama mutanen ne bayan da aka bibiyi nambar wayar da aka yi amfani da ita wajen neman a biya kuɗin fansa na ₦10,000..

“Waɗanda ake  zargin sun haɗa da Aminu Abdullahi mai shekaru 30 mazaunin Gold and Base dake yankin Rayfield a ƙaramar hukumar Jos South sai kuma Suleiman Muhammad daga Dutsen Kura a karamar hukumar Bassa an kama su ne a wajejen Gold and Base ranar 5 ga watan Nuwamba da misalin ƙarfe 12:45 na rana sakamakon cikakken bincike da jami’an tsaron suka yi,” a cewar mai magana da yawun rundunar ƴan sandan.

A lokacin gudanar da binciken ne wanda aka yi garkuwa da shi ya gane Suleiman Muhammad a cikinsu.

More from this stream

Recomended