
Akalla wasu mata biyar aka ba da rahoton sun mutu bayan da kasa ta ruguzo kansu a wani haramtaccen wurin hakar ma’adanai dake karamar hukumar Paikoro ta jihar Niger.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro lamarin ya faru ne da misalin karfe 06:30 na yammacin ranar Litinin a kauyen Budu..
Mutanen da kasar ta ruguzo kansu sun hada da Faridat Mustapha, Farida Sule, Khadijat Abdullahi da Zainab Usman.
“Jami’an tsaro sun ziyarci wurin inda aka zakulo mutanen aka garzaya da su Babban Asibitin Paiko,” a cewar Makama.
“Abun baÆ™in ciki ana zuwa likitoci suka tabbatar da sun mutu.An ajiye gawarwakin su a dakin ajiye domin gudanar da binciken musabbabin mutuwarsa.”
Majiyar ta ce ana cigaba da gudanar da bincike tare da gargagadin al’umma kan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba dake jefa rayukansu cikin hatsari.