
Rundunar yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutane biyu da ake zarginsu da hannu da yin garkuwa da matar Hakeem Odumosu tsohon mataimakin babban sufeton ƴan sanda.
A wata sanarwa mai magana da yawun rundunar,Muyiwa Adejobi ya ce mutanen da aka kama sun haɗa da Agbojule Smart da kuma Keleke Michael an kama su ne da tsakar daren ranar Alhamis lokacin da suke ƙoƙarin barin jihar Lagos.
Adejobi ya ce mutanen sun faɗi cewa suna daga cikin gungun mutane huɗu da suka ɗauke matar ranar 16 ga watan Janairu a jihar Ogun.
Ya ƙara da cewa jami’an ƴan sanda sun ƙwato naira miliyan ₦2,255,000 wanda na daga cikin kaso na kuɗin fansar da suka karɓa da kuma bindigogi biyu ƙirar gida guda 2 da kuma harsashi 11.
Kama mutanen da aka yi na zuwa ne kwana guda bayan da rundunar ƴan sandan ta sanar da kuɓutar da matar Odumosu.
A cewar ƴan sandan an ceto matar ne bayan da aka yi musayar wuta da masu garkuwar a maɓoyarsu. An kashe biyu daga cikinsu nan take a yayin da biyu suka samu nasarar tserewa.
Adejobi ya ce yan sandan sun gano bindiga ƙirar AK-47 guda 4, bindigogi ƙirar gida guda uku da kuma harsashi iri daban-daban da kuma kuɗin fansa naira miliyan 10