Wasu makusantan El-Rufai sun fice daga jam’iyar APC

Wasu daga cikin makusantan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru Elrufa’i sun sanar da ficewarsu daga jam’iyar APC.

Mutane huɗu da suka rike mukamin kwamshinan a gwamnatin ta El-Rufai suka sanar da ficewarsu daga jam’iyar biyo bayan sauya sheƙar da El-Rufai ya yi daga APC ya zuwa jam’iyar SDP a ranar Litinin.

Waɗanda suka sauya shekar a baya-bayan nan sun haɗa da Ibrahim Hussaini kwamishinan noma, Aisha Dikko kwamishiniyar shari’a, Amina Baloni kwamishiniyar lafiya, da  Halima Lawal kwamshiniyar ilimi da kuma tsohuwar shugabar ma’aikatan jihar f Head of , Hajiya Bari’atu Mohammed.

Duk da cewa mutanen basu bayyana jam’iyar da za su koma ba wasu majiyoyi na bayyana cewa za su tsallaka ne ya zuwa jam’iyar SDP su haɗe da El-Rufai.

Ficewar mutanen daga jam’iyar ya jefa damuwa a cikin jam’iyar APC reshen jihar Kaduna inda ake ganin El-Rufai a matsayin wani babban jigo a siyasar jihar dama yankin arewa.

More from this stream

Recomended