Wasu Kungiyoyi Za Su Taimakawa Manoman Tumatur A Nigeria

[ad_1]

Kungiyoyin da suka kuduri taimakawa manoman tumatir a Nigeria sun hada da Farm Radio International da gidauniyar Rockefeller da Access Agriculture da PYXERA GLOBAL da kuma Techno serve.

A yayin taro da manema labarai a nan Kano jiya Alhamis, bayan kammala taron bita ga wasu manoman tumatir da kuma jami’ai daga wasu kafofin labarai na Kano, kungiyoyin sun ce bincike ya nuna cewa kashi 40% na doya da dangoginta a yankin sahara na Afrika da 50% na adadin kayan marmari, da tumatiri da dangoginsa, suna salwanta bayan nunar su a gona kafin su kai lokacin sarrafawa a tukunya.

Kungiyar farm Radio international wadda ta maida hankali wajen aikin dakile asarar da manoman tumatir keyi a kasashen Nigeria da Tanzania da kuma Kenya, na kawance da sauran kungiyoyi domin cimma wannan buri.

Kungiyar PYXERA GLOBAL na cikin irin wadannan kungiyoyi kuma Malam Awal Salisu na cikin jami’an dake tafiyar da ayyukan kungiyar a nan Nigeria. Awal Salisu na cewa sun haka kai ne domin sun fahimci cewa wajibi ne a wayar da kawunan manoman domin su rage asarar da suke tafkawa saboda jahilci. Kafar rediyon da kungiyar ke anfani dashi za’a yada matakan wayar da kai domin mutane da dama su gane. Ana son a hada karfi da karfi a tabbatar cewa manoma sun himmatu.

Shi kuwa, Malam Dahiru Mukhtar babban Jami’i a kungiyar Tecnoserve yace yanzu haka aikin karfafa gwuiwar manoman tumatir a Nigeria ya maida hankali a jihohi guda biyar inda ya ce suna aiwatar da ayyukansu. Jihohin sun hada da Kano, Kaduna, Katsina, Jigawa da Plato. Za su duba duk matslolin da suka hana manoman tumatir cin ribar aikinsu.

Wannan yunkuri da kungiyoyin ketare keyi na zuwa a dai-dai lokacin da manoman timatir ke nuna damuwa kan yadda wasu hukumomin gwamnati ke kin aiwatar dokar haramta shigo da markadadden tumatir cikin najeriya daga ketare.

A cewar Alhaji Sani Danladi Yadakwari sakataren kungiyar manoman tumatir a Nigeria ko a wannan shekara sun yi asara da ta wuce Naira biliyan goma.

A saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...