Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya bayyana cewa akwai mutane da ba za su taɓa yafe wa Tinubu ba saboda matakan da ya ɗauka na cire tallafin man fetur da kuma barin Naira ga kasuwa ta yi halinta.
Sunday Dare ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi ranar Asabar a shirin Mic On Podcast, inda aka tambaye shi wane “zaki” ne Shugaba Tinubu ya tayar da shi.
A cewarsa: “Dubi sauye-sauyen da ake yi yanzu. Ka ɗauki sashen mai. Wasu daga cikinsu ba a cika maida hankali a kansu ba.
“Ka san yawan mutanen da ke cin gajiyar tsarin tallafin mai? ‘Yan Najeriya daga sassa daban-daban na ƙasar.
“Ba na son in kira su ‘oil mafia’, amma mun san akwai waɗanda suka yi ƙoƙarin dakatar da cire tallafin.”
Kan batun sakin Naira, Dare ya ce: “An samu sabbin attajirai a cikin ƴan watanni kaɗan karkashin gwamnatin da ta gabata. Bambancin farashin canji ya haifar da babbar dama.
“Tinubu yana da zabin barin hakan ya cigaba. Da ya yi hakan, kowa zai ci gajiyar hakan. Amma ya kawo ƙarshen hakan.”
Ya ƙara da cewa: “A cikin wannan tsari, akwai mutane a yau da ba za su taɓa yafewa Tinubu ba kan yadda ya saki Naira da cire tallafin man fetur da kuma na kuɗin waje.”
Dare ya bayyana cewa matakan na Tinubu sun shafi wasu ƙungiyoyi da mutane masu ƙarfi a tattalin arziki, waɗanda ke kallon sauye-sauyen da ke gudana a matsayin barazana ga ribarsu.
Wasu Ba Za Su Taɓa Yafe Wa Tinubu Kan Al’amarin Naira Da Cire Tallafin Man Fetur Ba – Inji Sunday Dare
