Wasu ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karɓar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin karbar kayan abinci da gwamnatin jihar ta raba a wani bangare na tallafin lalacewar tattalin arziki.

Wadanda lamarin ya rutsa da su, kuma wadanda har yanzu ba a bayyana sunayensu ba, abin ya rutsa da ne a safiyar Juma’a, wanda ya yi sanadiyyar jikkatar su.

Wata majiya ta bayyana cewa daliban da suka mutu mata ne, yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban a yayin da lamarin ya faru a dandalin Convention dake harabar jami’ar.

More News

Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin...

Mutanen Isra’ila sama da rabin miliyan sun tsere saboda yakin Gaza

Mutanen Isra'ila sama da rabin miliyan ɗaya ne suka fice daga ƙasar kuma ba su koma ba a watanni shida na farkon yaƙin Isra'ila...

Gwamnati za ta fara biyan ma’aikata naira 30,000 mafi ƙarancin albashi a Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya sanar da cewa za su fara aiwatar da tsarin mafi ƙarancin albashi naira 30,000 ga ma'aikatan jihar...

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...