Wasu matasa ‘yan Najeriya hudu sun kirkiro wani janareta mai amfani da litar fitsari don samar da wutar lantarki ta sa’o’i shida.
Ƴan matan – Duro-Aina Adebola, Akindele Abiola, Faleke Oluwatoyin, da Bello Eniola sun baje kolin kere-keren nasu ne a taron shekara-shekara na Maker Faire Africa, da aka gudanar a Legas.
Abiola, Oluwatoyin da Eniola sun fito da wata hanya mai amfani don aiwatar da wannan tunanin kuma gidaje da yawa za su iya amfani da shi.
RusselSmith, babbar jami’ar samar da Integrated Energy Solutions ta bayyana hakan, inda ta kara da cewa Adebola, ‘yar shekara 14, ta ce manufar yin amfani da fitsari wajen samar da wutar lantarki ta faro ne a lokacin da ta karanta labarin wasu mutane biyar da suka rasa rayukansu.
Ta ce sun mutu ne sakamakon gubar carbon monoxide yayin da suke shakar hayakin da ke fitowa daga janaretonsu a lokacin da suke barci.