Wani Ya Hau Turken Sadarwa Domin Nuna Fushinsa Ga Buhari

A wani mataki na nuna fushinsa, wani matashi mai suna Nura Iliyasu mazaunin jihar Kaduna ya hau turken wayar salula a Abuja domin nuna bore ga gwamnatin Buhari.

Da waikilin Muryar Amurka ya tambaye shi abin da ya sa ya yi hakan, sai ya ce lokacin neman zabe an yi masu alkawarin za’a cece su daga halaka da zaran an kafa gwamnati, amma ba haka lamarin ya ke ba yau.

A cewar shi, sun tura kati sun kashe kudi amma da gwamnatin ta zo ta kara masu kudin mai.

Yayin da yake neman zabe Shugaba Buhari wai har kuka ya yi saboda ana sayarwa ‘yan Najeriya man fetur sama da Nera 40.

Ya yi ikarin cewa shugaba Buhari ya yi korafi kan yadda ake sayarwa ‘yan Najeriya da mai fiye da Nera 40, lamarin da ya kwatanta a matsayin cuta ce.

Amma sai ga shi ana sayar da mai fiye da Naira 200, inji matashin.

Farashin dala kafin ya hau gwamnati 137 amma yanzu 360 ko fiye da haka.

Nura ya ci gaba da cewa duk kasashen OPEC babu inda matatun mai ba sa aiki sai Najeriya.

Nura har ila yau ya yi korafi kan yadda wasu da ya kira “‘yan koro” suka hada kudi suka saya mai fom domin ya tsaya takara.

Yau She Matashin Zai Sauka Daga Kan Turken?

Nura ya ce zai yi kwanaki bakwai akan turken yana mai cewa yawancin mutane sai sun yi bara su ci abinci.

Ya kara da cewa, ruwa, shi zai zama abincinsa kuma ruwan da ya zo da shi zai sha.

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...