Wani mutum ya yi wa abokinsa da ya damfara  miliyan 30 yankan rago

Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta kama wani mutum mai suna, Efe Onoetiyi da ake zarginsa da kashe abokinsa, Paulinaus Okon bayan da ya cinye masa kuɗinsa miliyan 30.

Da yake magana da manema labarai ranar Litinin lokacin da yake nunawa ƴan jarida wanda ake zargin, kwamshinan ƴan sandan jihar,Abaniwonda Olufemi ya ce wanda ake zargin ya haɗa kai da wasu mutane uku wajen aikata laifin.

Sauran waɗanda ake zargin sun haɗa da Okeimute Gaga, Lawrence Joseph,  Sunday Ikpeba.

Olufemi ya ce Onoetiyi ya amsa laifin kisan Okon bayan da ya barnatar da naira miliyan 30 da marigayin ya bashi domin ya saya masa gida.

Kwamishinan ya ce wanda ake zargin ya yi abokin nasa tallan wani gida da aka yi masa kuɗi naira miliyan 30 inda shi kuma abokin ya biya kuɗin miliyan 10 sau uku a lokuta daban -daban.

Amma kuma sai Onoetiyi ya kashe kuɗin ta hanyar sayan fili da kuma motar hawa.

Da iyalan marigayin suka tambaye shi ko sun haɗu sai ya ce sun daɗe basu haɗu ba amma su kawo kuɗi ₦500,000 aje gurin boka ayi maganin gano inda ya shiga.

More from this stream

Recomended