Wani mutum ya tsallake rijiya da baya a jihar Lagos

Wata kwantenar kaya mai tsawon ƙafa 40 ta faɗo kan wata mota a yankin Mile 2 dake jihar Lagos.

A wata sanarwa ranar Litinin hukumar LASTMA dake lura da zirga-zirga ababen hawa a jihar ta ce an samu nasarar zaƙulo  direban motar da ransa daga ƙasar kwantenar.

Adebayo Taofiq mai magana da yawun hukumar ta LASTMA ya ce an garzaya da direban motar ya zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.

“Biyo bayan aikin ceto da aka ƙaddamar an samu nasarar ciro mota ƙirar Toyota Camry daga ƙasan kwantenar,” a cewar Taofiq.

Hatsari irin wannan abu ne da ya zama ruwan dare a birnin na Lagos inda a lokuta da dama yake zuwa da asarar rayuka.

More from this stream

Recomended