Wani mutum ya kashe mahaifiyarsa bayan ya caka mata wuka

Wani mutum dan shekara 30 mai suna Nwabueze Anakan ya kashe mahaifiyarsa ta hanyar caka mata wuta kafin daga bisani ya cika wandonsa da iska a cewar yan sanda.

Lamarin ya faru ne a Oraifite dake karamar hukumar Anambra ta kudu dake jihar Anambra.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Haruna Muhammad cikin wata sanarwa ya ce an kai rahoton faruwar lamarin a ofishin yan sanda na Oraifite ranar Talata da misalin karfe 12 na rana kuma da safiyar ranar ne aka zargi Anaka da cakawa mahaifiyarsa wuka mai suna, Grace Amaka yar shekara 50.

Muhammad ya ce jami’an yan sanda dake gudanar da bincike sun isa wurin da abin ya faru inda suka dauke ta zuwa asibiti anan likitoci suka tabbatar da mutuwarta.

More from this stream

Recomended