
An yankewa wani mutum hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan gyaran hali ba tare da zaɓin tara ba bayan da kotu ta same shi da laifin sare yatsan budurwarsa bayan da ya sameta ita da wani a ɗaki.
Mutumin mai suna Mas’ud Yusuf wanda yake zaune a kasuwar Dei-Dei an gurfanar da shi a gaban kotun majistire dake zaman ta a Jiwa babban birnin tarayya Abuja inda aka tuhume shi da yin lahani tare da farma ƙawarsa mace laifin da ya saɓa da sashe na 247 dana 265 na kundin penal code.
Mai shari’a Linda J.C ita ta zartar da hukuncin.
Tun da farko mai gabatar da ƙara, JN Atinko ya faɗawa kotun cewa wata mata mai suna Fatima Muhammad Lawal ta kai ƙorafi ofishin ƴan sanda na “A” dake Dei-Dei ranar 11 ga watan Janairu inda take zargin wani mutum da yanke mata yatsa ɗaya tare da yi mata rauni a ɗaya a lokacin da tayi ƙokarin kare wuyanta lokacin da wanda ake tuhuma ya kai mata sara da adda.
Ya ce dogaro da bayanan matar mutumin ya ɗauki matakin ne sakamakon haushin da ya ji bayan da ya same ta da ɗaya daga cikin abokansa a ɗaki.
Yusuf ya amsa laifinsa amma ya roƙi kotu da ta yi masa afuwa.