Wani Makeken Jirgin Sojin Amurka Ya Yi Hatsari A Iraƙi

Rundunar sojin Amurka ta tabbatar da cewa wani jirginta na soji ya yi hatsari a yammacin ƙasar Iraƙi.

Jirgin na KC-135 ya faɗo ne bayan wani abin da jami’an soji suka bayyana a matsayin “hatsari” da ya shafi jirage biyu.

A cikin wata sanarwa, rundunar sojin Amurka ta ce ana ci gaba da aikin ceto a yankin da lamarin ya faru.

Sojojin sun kuma bayyana cewa hatsarin ya auku ne a wani yanki da ba na maƙiya ba.

“Lamarin ba ya faru ba ne a yankin da ake yaƙi ko kuma musayar wuta,” in ji sanarwar.

More from this stream

Recomended