Wani karamin jirgin sama ɗauke da ministan wutar lantarki ya yi hatsari a Ibadan

Wani karamin jirgin haya da ya tashi daga Abuja zuwa Ibadan ya faɗi a lokacin da yake sauka a filin jirgin saman Ibadan.

Mitoci kaɗan ya rage jirgin ya kara kan titinsa hatsarin ya faru.

Jirgin mallakin kamfanin Flint Aero na ɗauke da mutane 10 lokacin da hatsarin ya faru.

Babu rahoton asarar rayuka a hatsarin amma kuma wasu sassan jirgin sun ɓaci bayan da ya tsaya a cikin dajin dake zagaye da titin sauka da tashin jiragen sama na filin jirgin.

Wasu rahotanni na cewa a cikin mutanen dake cikin jirgin akwai ministan harkokin wutar lantarki, Adebayo Adelabu.

More from this stream

Recomended