Wani Hari Da Akai Kai Ya Kashe Akalla Mutane 23

Bayanai dai na nuni da cewa a karshen mako ne wasu mahara suka kai harin a wasu kauyuka na yankin Numan inda aka samu asarar rayuka da kuma kona gidaje yayin da wasu kawo yanzu ba’a ma san inda suke ba.

Sodom Tayedi ita ke wakiltar yankin na Numan a majalisar dokokin jihar Adamawa ta ce yanzu haka sun binne fiye da mutum 23,ciki har da mata. A cewarsu bayan da suka binne mutanen yanzu sun shiga neman wadanda ba’a san inda suke ba.

Dangane da matan da tun farko ta ce an yi garkuwa dasu Sodon Tayedi ta ce an saki wasu kana kuma an kashe wasu.

To sai dai kuma,mukaddashin kakakin rundunan yan sandan jihar Adamawa,DSP Habibu Musa Muhammad,wanda ya tabbatar da harin da aka kai a yankin na Numan ya musanta batun garkuwa da matan,to amma kuma yace suna kokarin zakulo maharani dake kai hare haren. Ya ce ba su samu labarin yin garkuwa da mata da kananan yara ba, baicin wadanda suka gudu suka shiga wasu lunguna. A cewarsa wasu sun dawo. Yan sanda na ci gaba da bincike.

Wannan na zuwa ne yayin da shugabanin al’umman yankin na Abbare ke musanta zargin cewa suke kai wadannan hare hare,batun da suka ce wasu ne ke kokarin hadasu fada da al’umman Bachama da suka dade suna huldar zumunci. Ali Madugu Abbare ya ce labarin da suka ji bai yi masu dadi ba na cewa su ne suke kai hari kauyukan Bachama dake Adamawa. Ya ce su da Bachama basu da tashin hankali. Sun dade suna abinsu tare

Itama dai rundunan yan sandn jihar Taraba ta bakin kakakinta ASP David Misal ta musanta batun yin garkuwa da matan a Abbare ta kuma bayyana matakan da aka dauka a yankin. David Misal ya ce akwai jami’ansu a Abbare soboda haka da wuya a ce mutanen yankin suka kai hari cikin Adamawa ba.

More News

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...