Wani gini ya ruguzo kan mutane a Abuja

Mutane da dama ne suka makale a kasan ɓaraguzan wani gini da ya ruguzo a yankin Sabon Lugbe dake birnin tarayya Abuja.

Wasu bayanai sun bayyana cewa ginin ya ruguzo ne da yammacin ranar Asabar.

Wasu fefayen bidiyo da aka wallafa a soshiyal midiya sun nuna yadda mutane suke aikin ceton mutanen da abun ya rutsa da su.

“Mutane suna ƙasan ɓaraguzai gini ne da ake kan aikinsa.”

“Muna kira ga gwamnati da hukumomin da abun ya shafa da su zo su ceto mutanennda suka maƙale a cikin ɓaraguzan ginin,”a cewar wani dake magana da manema labarai a wurin.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa daga hukumomi kan yawan mutanen da abun ya rutsa da su.

Rushewar ginin na zuwa ne ƴan kwanaki kaɗan bayan da wani ya ruguzo a jihar Lagos.

More from this stream

Recomended