Rundunar ƴan sandan jihar Yobe ta sanar da kama Haruna Muhammad mai shekaru 40 wanda aka yi ittifakin cewa shi ne shugaban wasu gungun ƴan ta’adda da suka yi ƙaurin suna.
Mista Dungus Abdulkarim mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya faɗawa manema labarai dake jihar cewa sashen tattara bayanan sirri na rundunar ne ya samu nasarar kama shi.
A cewar Abdulkarim wanda aka kama na da hannu wajen farma ƙauyuka da garuruwa dake maƙotaka da jihar ta Yobe ta hanyar damunsu da kira waya yana buƙatar kuɗi ko kuma wasu kaya masu muhimmanci.
“Wani mutum daga ƙauyen Siminti ya kai rahoton cewa Muhammad ya buƙaci a biya shi Naira miliyan 3 ko kuma ya kashe shi da iyalansa,”
A ranar 16 ga watan Yuni ne aka kama Muhammad a ƙauyen Nangilan dake ƙaramar Tarmuwa ta jihar.