Rundunar Ƴan Sandan jihar Lagos ta ce jami’an ta sun kama wani mai suna Ifeanyi Okonkwo da ake zargi da sace wayar hannu a wani wurin cin abinci dake Alausa a Ikeja.
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin rundunar ta ce wanda ake zargin ya ziyarci wurin cin abinci a ranar 7 ga watan Nuwamba domin sayen abinci amma ya bige da satar waya kirar Samsung A15 ta wani mai sayen abincin.
Sanarwar ta ce jami’an kar ta kwana na rundunar su ne suka kama Okonkwo a gidan cin a ranar 5 ga watan Disamba.
A cewar sanarwar a wancan lokacin da ya yi satar bai san cewa na’urar CCTV ta ɗauki bidiyonsa ba.
Rashin sanin haka ne ya sa shi sake komawa gidan abincin aka kuma yi sa’a suka gane shi su ka kuma yi saurin sanar da jami’an ƴan sanda dake kusa.
Tuni rundunar ta gano wayar a hannun wanda aka sayarwa a yayin da shi kuma aka miƙa shi gaban kotu.