Wani ɗan sandan Najeriya ya kashe kansa bayan ya hallaka abokin aikinsa bisa kuskure

Wani dan sanda a rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, Insifekta Nelson Abuante, ya kashe kansa bayan da rahotanni suka ce ya harbe abokin aikinsa, Monday Gbaramana.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata a Nyogor-Lueku da ke cikin karamar hukumar Khana a jihar, inda jami’an biyu wadanda ke aiki da sashen Taabaa na rundunar ‘yan sanda suka je suka kama wani da ake zargi sakamakon korafin da mahaifiyarsa ta kai.

An rawaito cewa rikicin ya fara ne lokacin da wanda ake zargin, Akere Akpobari ya ki amincewa da yunkurin kama shi.

Tirjewar tasa ta haifar da hatsaniya, lamarin da ya sa Abuante ya harbi Gbaramana bisa kuskure, nan take aka garzaya da Gbaramana asibiti.

Sai dai an yi zargin cewa motar da ta kai su asibiti man cikinta ya kare, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Shi kuwa Abuante, ya harbe kansa da bindigar sa bayan an tabbatar da mutuwar abokin aikinsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin.

More from this stream

Recomended