Wanda aka zaba ya zama minista daga Kaduna ya faɗi a gaban majalisa

Mutumin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya turawa majalisar dattawa domin tantancewa a matsayin minista ya yanke jiki ya faɗi a majalisa.

Balarabe Abbas Lawal shi ne aka zaba ya zama minista daga jihar Kaduna bayan da majalisar dattawa taki amincewa da Elrufai.

Abbas ya fadi ne dai-dai lokacin da ya kammala jawabi akan tarihinsa da karatun da yayi.

Shugaban majalisar dattawan, Godswill Akpabio ya yi gaggawar kiran likita domin su duba halin da yake ciki.

More from this stream

Recomended