Wadanne Kalubale Ke Gaban Sabon Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya? – AREWA News

Sufeton ‘yan sandan Usman Alkali Baba ya dai yi alkawarin gudanar da aikin nasa me tare da hadin gwiwar jama’ar da ke zaune awuraren da ‘yan ta’addan ke aikata barnasu da kuma cin karansu ba babbaka.

Masana a harkar tsaro dai sun kalubanci sabon mukaddashin ‘yan sanda kan ya maida hankali kan kwantar da matsalolin rashin tsaro da ke karuwa a sassa daban-daban na kasar, suna masu cewa yana cikin tsaka mai wuya domin rashin kayan aiki da wadataccen kudi na kaddamar da aiki.

Wani masani kan harkokin tsaro Yuhuza Ahmad Getso, ya bayyana cewa rashin kayan aiki na daga cikin babban matsalar da sabon mukaddashin Sufeton zai fara fuskanta a yayin gudanar da aikinsa.

Karin bayani akan: Usman Alkali Baba, IGP, Nigeria, da Najeriya.

Sai dai a cewar sabon sufeton ‘yan sandan IGP Usman Alkali Baba, a karkashin jagorancinsa, rundunar ‘yan sanda za ta kawo sauye-sauye da matakai don yaki da matsalar tsaro a Najeriya.

A na shi bangaren, masanin tsaro Kabiru Adamu, a shawarar da ya bayar ga sabon Sufeton, ya ce akwai dokoki da abubuwa da yawa da ke cikinsu da ya kamata a yi amfani da su.

(Daily Post)

Related Articles