Uzodinma ya amince da biyan naira 40,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya amince da karin mafi karancin albashi ga ma’aikatan jihar zuwa 40000 domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Uzodimma lokacin da yake jawabi ga yan majalisar zartarwar jihar ya ce halin tattalin arziki da ake ciki yanzu sanadiyar cire tallafin man fetur na yin illa ga jama’a sosai.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Oguwike Nwachukwu ya fitar Uzodimma ya ce gwamnatinsa za ta ba da bashi mai sauki, tallafin kudi, irin shuka da kuma kayan noma ga manoman da suka da ce a jihar.

Gwamnan ya ce akalla karin zai bawa ma’aikatan damar sayan kayayyakin bukatun yau da kullum.

More from this stream

Recomended