TY Danjuma ya nemi ƴan Najeriya su kare kansu

Theophilus Danjuma tsohon ministan tsaro ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ɗauki alhakin kare lafiyarsu.

Da yake magana a ƙaramar hukumar Takum ta jihar Taraba, Danjuma  ya ce yawan garkuwa da mutane da kuma hare-hare da ake samu a yan kwanakin nan ya nuna aƙarara cewa baza a iya dogara da gwamnatin kadai ba domin ta bawa al’umma kariya.

“Nasan muna da matsaloli da dama ciki har da tsaro a ƴan kwanaki biyu ko uku da suka wuce,” ya ce 

“Mun fuskanci garkuwa da mutane za a cigaba da fuskantar barazanar yin garkuwa da mutane har sai  kowanne daga cikin mu ya tashi mun kare kan mu,”

” A fili yake ƙarara gwamnati ita kaɗai baza ta iya ba. Nayi kashedi tun dadewa a wani jawabi da nayi a Wukari cewa dole mutanen mu su shirya kare kansu.”

“Wancan gargadin yana nan har yanzu kamar  yadda nayi shi a wancan lokacin, ” .

More from this stream

Recomended