- Daga Ozge Ozdemir
- BBC Turkish
Darajar kudin Turkiyya ta fadi da kaso 55 cikin 100 a kan dala a wannan shekarar, amma kuma shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan, sam bai damu ba.
Kudin kasar wato lira ya fadi a makon da ake ciki, amma sai gashi shugaban kasar mafi dadewa a wani taron manema labarai ya bayyana rage ruwa.
Abin tambayar a nan shi ne me yasa Mr Erdogan ya ke kara sanya kasar cikin matsala? baya ga matsalolin da take ciki da suka hada da hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi ga kuma talauci.
Dalilin da ya sa kudin Turkiyya lira ya rage daraja shi ne sabbin tsare-tsaren tattalin arzikin da shugaban kasar ya fitar na rage kudin ruwa da kuma fitar da kayayyaki domin su yi gogayya da kudaden ketare.
Ga wasu masana tattalin arziki, idan aka samu hauhawar farashin kayayyaki to yadda za a shawo kansa shi ne sai a kara kudin ruwa, to amma ga Mista Erdogan, yana yi wa kudin ruwa kallon wani mugun abu da ke karawa masu karfi da kuma karawa talaka talauci.
Sevim Yildirim, ta shaida wa BBC cewa, a yanzu farashin komai ya tashi hatta a kasuwar sayar da kayan marmari, ta ce abu ne mai wuya ka iya ciyar da iyalinka sau uku saboda tsadar kayayyaki.
A duniya baki daya ana fama da hauhawar farashin kayayyaki, sannan manyan bankunan kasashe kuma na kara kudin ruwa. To amma banda Turkiyya saboda Mista Erdogan ya yi amanna cewa za a samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki.
A cikin shekaru uku da suka gabata, Mista Erdogan ya kori shugabannin babban bankin kasar uku, sannan a wannann makon ne ya sauya ministan kudin kasar. A don haka darajar lira kuwa na ci gaba da faduwa.
Tattalin arzikin Turkiyya ya dogara ne kacokan a kan shigo da kayayyaki domin samar da kayayyaki na cikin gida da suka hada da abinci da kayan sawa, wanda hakan ke tasiri matuka ga tashin dala ke yi a kan lira.
Kamar misali tumatir, idan ana son a samar da tumatir mai kyau a kasar to dole masu noman tumatirin su sayi taki da gas din da aka shigo da su cikin kasar.
A watan Agusta, farashin tumatir sai da ya karu da kaso 75 cikin 100 idan aka kwatanta da bara war haka.
Sadiya Kaleci, ta kasance tana noman inibi a Pamukova, wani karamin gari mai nisan sa’oi uku daga Santanbul, an tambayeta ta yaya za ta samu kudi a wanann sana’a? ta ce suna sayar da kayayyaki da sauki a wajensu, amma kuma suna sayen abubuwa da tsada, kamar man diesel da taki da makamantansu.
Wata manomiya Feride Tufan, ta yi korafin cewa hanyar da take samun kudin ita ce sayar da kadarorinta wajen biyan bashi, ta ce kamar gona mukan sayar don mu biya bashi, to amma idan muka sayar da komai zamu dawo ba mu da komai kuma.
Ana ta samun sauye-sauye a kudin Turkiyya abin da ke sa farashin kayayyaki ke canjawa a kullum. Hakan Ayran, wani dan kasuwa ne ya ce ya rage kashe-kashen kudin da yake saboda idan har kana so ka rinka biyan ma’aikatanta to dole ka rage ciki.
Ma’aikatan manyan shaguna sun rinka wallafawa a shafukansu na sada zumunta irin yadda farashin kayayyaki suka tashi.
‘Yan kasuwar sun wallafa yadda farashin blue band da man zetun da ganyen shayi da gahawa da kuma tolet paper ya tashi.
Wani mai gidan beridi a Turkiyya Izmir, ya yi bayanin yadda farashin biredinsa ya tashi saboda farashin kayayyakin hada biredin kamar fulawa da siga da dai sauransu ya tashi.
Bashin da ake ciwowa daga kasashen waje babbar matsala ce ga bangarori masu zaman kansu sannan yawancin kamfanoni su kan samu riba idan suka boye kayayyaki mai makon su sayar da su saboda yadda darajar kudin kasar ke sauyawa.
An samu dogayen layuka a wajen gidajen mai da kuma wajen ofisoshin kananan hukumomi inda ake bayar da biredi mai rahusa.
Tuni jam’iyyun adawa suka yi kira da a gudanar zabe da kuma zanga zanga.
A yanzu matasa kan yi amfani da shafukan sada zumunta wajen bayyana rashin dadinsu game da yadda al’amura ke tafiya a gwamnati.
A yanzu a kan samu matashi daya cikin biyar da baya aiki, abin ma ya fi muni ga mata.
Matsalar rashin aiki
Turkiyya ta kasance kasa ta hudu a duniya da take fama da matsalar aikin yi a tsakanin matasa da kuma rashin ilimi.
Idan matasan Turkiyya suka kwatanta kansu da takwarorinsu na wasu kasashen su kan ce kaico, saboda akwai wagegen gibi.
Wani matashi dan shekara 18 a Turkiyya, ya ce matashi kamarsa a Amurka ko wata kasar turai zai iya sayen wayar Iphone da albashinsa, amma, su a Turkiyya koda suna aiki ba za su iya saya ba.
A zaben kasar da za a yi a 2023, akwai ƴan Turkiyya miliyan 9 da suka cancanci su kada kuri’a, a don haka akwai rawar da matasa za su taka sosai.
Wani hoton bidiyo da ya rinka yawo a kafar sada zumunta a kasar ya nuna yadda wata mata ke yabon Shugaba Erdogan, amma kuma sai ga shi ‘yarta mai shekara 8 tana adawa da shugaban.
Yawancin tattalin arzikin Turkiyya na habaka ne ta hanyar kudaden da gwamnati ke kashewa da kuma gine-gine masana’antu.
(BBC Hausa)