Tsohon shugaban Najeriya, Gowon, ya yanki jiki ya fadi a wurin taron jana’iza.

Toshon shugaban mulkin soja,Janar Yakubu Gowon ya yanke jiki ya fadi a wurin jana’izar David Akpodiete Ejoor da aka gudanar Ovwor-Olomu dake karamar hukumar Ughelli South a jihar Delta.

Lamarin ya faru ne a kusa da kabarin dai-dai lokacin da ake gabatar da addu’o’i.

Manyan jami’an soja dake wurin sun garzaya da tsohon shugaban kasar zuwa cikin wata rumfa ta musamman domin gaggauta farfaɗo da shi ya yin da tsohon gwamnan jihar,James Ibori da kuma gwamna mai ci Ifeanyi Okowa suka garzaya ciki domin tabbatar da cewa ya farfado.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya Nan ya rawaito cewa motocin ɗaukar marasa lafiya ta sojan rundunar sojan Najeriya da kuma ta gwamnatin jihar sun garzaya bakin wurin domin jira ko ta kwana.

Bayan jimawa kadan an hango Okowa da Ibori na fitowa daga cikin rumfar alamun dake nuna cewa ya farfaɗo.

More from this stream

Recomended