Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana alhininsa tare da aika sakon ta’aziyya ga Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, dangane da jerin munanan rashe-rashe da suka auku a jihohin Oyo, Anambra, da Babban Birnin Tarayya (FCT), inda aka yi asarar rayuka da dama.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Buhari ya aika ta’aziyyarsa ga Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo, Gwamna Chukwuma Soludo na Jihar Anambra, da Ministan FCT, Nyesom Wike.
Ya kuma bukaci su isar da sakonsa na ta’aziyya da goyon baya ga iyalai da dangin wadanda suka rasa rayukansu a wannan bala’i, tare da fatan samun sauƙi cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Haka zalika, tsohon Shugaban ya mika sakon ta’aziyyarsa ga al’ummar Katolika da abin ya shafa a Abuja, yana mai addu’ar samun karfin hali ga dukkan masu jimamin wannan rashi.