
Adamu Maina Waziri, tsohon ministan yan sanda ya sanar da ficewarsa daga jam’iyar PDP.
Waziri wanda na daya daga cikin wadanda aka kafa jam’iyar PDP da su kuma mamba ne a kwamitin amintattun jam’iyar ya sanar da daukar matakin barin jam’iyar PDP a ranar Litinin a mazabar Dogo Tebo dake karamar hukumar Potiskum ta jihar Yobe.
Ya alakanta barin jam’iyar da halin da ake ciki a yanzu da kuma samawa kasar makoma kyau.
A cewar tsohon ministan shugabancin jam’iyar PDP da ake da shi a yanzu bai yi dai-dai da irin wanda ya dace da babbar jam’iyar siyasa ba.
Ya kara da cewa nan take ya koma jam’iyar African Democratic Alliance (ADC) nan take.
A yan makonni jam’iyar PDP ta fuskanci sauya sheka daga cikinta da wasu manyan yan siyasa su ka yi ya zuwa APC da ADC.