An zabi, Nentawe Yilwatda ministan ma’aikatar jinkai da yaki da talauci a matsayin sabon shugaban jam’iyar APC na kasa.

An sanar da zaben Nentawe a hukumance a ranar Alhamis a wurin taron kwamitin gudanarwar jam’iyar na kasa da aka gudanar a Abuja.
Jagororin jam’iyar APC sun taru a Abuja dominĀ fitarwa jam’iyar sabuwar alkibla gabanin zabukan shekarar 2027.
Yilwatda ya dare shugabancin jam’iyar ne a matsayin dan takarar maslaha da masu ruwa da tsaki a jam’iyar suka amince da shi.
Ya maye gurbin tsohon shugaban jam’iyar, Abdullahi Umar Ganduje wanda ya yi murabus a hukumance a ranar 27 ga watan Yuni.
Hope Uzodinma, gwamnan jihar Imo shi ne wanda ya gabatar da kudirin zaben Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyar kuma ya samu goyan bayan shugaban majalisar wakilai ta tarayya, Tajuddeen Abbas.
Sabon shugaban ya fito ne daga jihar Filato kuma shi ne ya yiwa jam’iyar APC takarar gwamna a zaben 2023.