Tsohon minista ya yanke jiki ya fadi ya mutu

Caleb Olubolade tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Bayelsa ya mutu yana da shekaru 70.

Olubolade wanda ya rike mukamin ministan ayyuka na musamman a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan ya mutu ranar Lahadi a yankin Apapa dake Lagos.

A cikin wata sanarwa da suka fitar Akinadewo Dayo Olubolade yayan marigayin sun bayyana cewa  tsohon ministan ya yanke jiki ya fadi ya mutu lokacin da yake buga wasan kwallon tenis.

“Ya tuka kansa ya zuwa wurin domin ya yi wasan tenis da maraice inda ya yanke jiki ya fadi lokacin da yake wasa. Kokarin da likitoci suka yi na farfado da shi ya ci tura,” a cewar  sanarwar.

An ayyana cewa ya mutu lokacin da aka kai shi asibitin sojan ruwan Najeriya na Obisesan dake Apapa.

More from this stream

Recomended