
Fred Chukwuelobe mataimaki kan harkokin yada labarai ga Chris Ngige ya ce tsohon gwamnan jihar ta Anambra yana hannun hukumar EFCC dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati.
A ranar Litinin ne wasu rahotanni suka bayyana a kafafen sadarwar zamani cewa wasu yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon gwamnan.
Chukwuelobe ya ce ya amsa kiran waya masu yawan gaske daga abokai da kuma yan jaridu dake neman karin haske kan garkuwar
“Ina ta amsa kiran waya a cikin yan sa’o’in da suka wuce daga abokai da kuma yan jarida dake neman sahihancin labarin dake yaduwa a gari cewa an yi garkuwa da mai girma, Dr Chris Ngige tsohon gwamnan jihar Anambra kuma tsohon ministan kwadago da ayyukan yi mai barin gado,” ya rubuta a shafinsa na Facebook.
“Ngige na hannun EFCC ba da dauka ko garkuwa da shi ba aka yi ba,”
Ya kara da cewa nan gaba kadan za su fitar da cikakken bayani kan lamarin.

