Hakkin mallakar hoto
Facebook / Maikanti Kachalla Baru
Tsohon Shugaban Kamfanin Mai na Kasa a Najeriya, NNPC Maikanti Kacalla Baru ya rasu.
Wata majiya daga iyalinsa ta tabatar wa BBC rasuwar Injiyan wanda aka haifa a 1959.
Shi ma shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari ya tabbatar da rasuwar a wani sakon ta’aziyya da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
An haifi marigayin a garin Misau na jihar Bauchi a 1959 kuma ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria 1982.
Maikanti Kacalla Baru ya rike mukamin shugaban kamfanin na NNPC daga 2016 zuwa 2019 bayan ya yi aiki a sassa daban-daban na bangaren mai a Najeriya.