Tsohon Gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi Ya Rasu

VOA

Rahotanni a Najeriya na cewa tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi ya mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus.

A cewar jaridar Premium Times, wani makusancin tsohon gwamnan mai suna Akin Alabi ne ya tabbatar da mutuwar tsohon gwamnan.

Bayanai na nuni da cewa, Mista Abiola Ajimobi ya mutu ne a bangaren kulawar gaggawa da ke wani asibiti a Legas bayan da ya fuskanci matsaloli da suka danganci Covid-19.

Ajimobi ya mutu yana da shekaru 70 a duniya.

Hakan na faruwa mako daya bayan da aka dinga yada cewa ya mutu, lamarin da ya janyo ‘yan uwansa suka fito suka musanta faruwar hakan.

Kafin rasuwarsa, Tsohon gwamnanThe 7 shine mataimakin shugaban Jam’iyar APC na kasa kafin kwamitin gudanarwa na jam’iyar ya rushe shugabannin a taron da aka gudanar yau a Abuja.

More from this stream

Recomended