
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom yanzu haka na ofishin hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati.
Hukumar EFCC ta gayyacin gwamnan ne domin ya amsa wasu tambayoyi kan yadda ya jagoranci jihar.
Ortom ya isa ofishin shiya na hukumar EFCC dake kan tatin Alor Gordon Makuri da misalin ƙarfe 10:08 na safe.
A yanzu za a iya cewa shi ne gwamnan farko da ya fara faɗawa komar EFCC cikin gwamnonin da suka kammala wa’adinsu na mulkin a ranar 29 ga watan Mayun 2023.