Tsare El-zakzaky : IMN ta mayar wa El-Rufa’i martani | BBC News

Hakkin mallakar hoto
AFP
Image caption

Kotu ta ba da umarnin sakin El-Zakzaky tun a shekarar 2016 amma a na ci gaba da tsare shi

A Najeriya, ‘yan kungiyar harkar Musulunci, ta mazhabar Shi’a, wato Islamic Movement of Nigeria, ta mayar da martani ga gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i,

Wannan na zuwa bayan da ta zargi gwamnan da yin kalaman cewa Shugaban kungiyar Sheikh Ibrahim Elzakzaky ba zai taba fita daga gidan yari ba matsawar yana mulkin jahar.

A cewar Ibrahim Musa shugaban dandalin yada labarai na kungiyar a Najeriya, El-Rufa’i ya yi kalamin ne a hira da wani gidan rediyo a ranar Juma’a.

Ibrahim Musa ya ce ga alama gwamnan yana da wani dalili na kashin kansa na ci gaba da tsare jagoransu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Ya kuma ‘kara da cewa kotu ta ba da umarnin sakin El-Zakzaky tun a shekarar 2016 amma gwamnati ta ci gaba da tsare shi babu dalili.

Masu fafutukar kare hakkin dan adam na yawan sukar gwamnati kan ci gaba da tsare sheikh Ibrahim El-zakzaky, suna cewa gwamnatin ba ta mutunta umurnin kotu tana kuma karan tsaye ga dokokin kasar.

Rikici tsakanin ‘ya’yan ‘kungiyar da hukumomin tsaro a Najeriya ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan musamman yan ‘kungiyar ta IMN.

More from this stream

Recomended