Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta ce ta kama wani mutum da aka bayyana da suna, Shu’aibu Yusuf.
A ranar Litinin Yusuf ya haifar da ruɗani bayan da ya hau ƙarfen turken hasumiyar yaɗa labarai ta gidan rediyo da talabijin na Aso dake Abuja domin nuna rashin jin daɗinsa kan matsin tattalin arziki da ake fama da shi a ƙasarnan.
A wani saƙo da ya rubuta ya kuma ajiye a ƙasa Yusuf ya ce zai sauko ne kawai idan aka kawo ƙarshen matsalar tsaro,matsin tattalin arziki da kuma matsalar yaran da basa zuwa makaranta.
Daga bisani ya sauko daga kan turken karfen bayan da Florence Wengieme muƙaddashiyar daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta birnin tarayya Abuja ta lallashe shi.
A wata sanarwa ranar Litinin, Josephine Adeh mai magana da yawun rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta ce yanzu haka Yusuf na tsare a hannun rundunar.
Adeh ta ce sashe na 327 na Kundin Manyan Laifuka ya ce duk wanda ya yi yunkurin kashe kansa za a iya gurfanar da shi gaban sharia ana kuma iya yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara ɗaya.