Tinubu zai wa ƴan Najeriya jawabi da safiyar ranar Talata

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu zai yi wa ƴan Najeriya jawabi a gobe ranar Talata da ƙarfe 07:00 na safe.

Bayo Onanuga mai bawa shugaban ƙasa shawara kan tsare-tsare da harkokin sadarwa shi ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Ya ce jawabin shugaban ƙasar wani ɓangare ne na bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun ƴanci daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Sanarwar ta shawarci gidajen talabijin da rediyo da su kasance da gidan talabijin na NTA da kuma gidan rediyon Najeriya domin samun damar watsa jawabin kai tsaye.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu domin bikin tunawa da ranar samun ƴan cin kan.

More News

Gwamnatin Enugu ta bayyana dalilin sanya haraji kan gawar mutane

Gwamnatin Jihar Enugu a ranar Lahadi tayi ƙarin haske kan matakin da ta ɗauka kan sanya haraji akan gawar mutane dake ajiye a ɗakin...

Ɗan tsohon gwamnan Kaduna Ahmad Makarfi ya rasu a hatsarin mota

Faisal Makarfi dan gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna Ahmad Muhammad Makarfi ya rasu. Faisal ya rasu a wani hatsarin mota da ya faru akan hanyar...

Ƴan sanda sun kama mutane 6 da ake zargi da kisan kai da fashi da makami a Gombe

Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta ce a cikin mako guda  jami'an ta sun kama wasu mutane 6 da ake zargi da aikata fashi...

Ƴan sanda sun kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Gyaran Hali na Maiduguri

Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce jami'an ta sun kama Kyari Kur ɗaya daga cikin ɗaurarrun da suka tsere daga gidan gyaran hali ...