Tinubu zai wa ƴan Najeriya jawabi da safiyar ranar Talata

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu zai yi wa ƴan Najeriya jawabi a gobe ranar Talata da ƙarfe 07:00 na safe.

Bayo Onanuga mai bawa shugaban ƙasa shawara kan tsare-tsare da harkokin sadarwa shi ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Ya ce jawabin shugaban ƙasar wani ɓangare ne na bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun ƴanci daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Sanarwar ta shawarci gidajen talabijin da rediyo da su kasance da gidan talabijin na NTA da kuma gidan rediyon Najeriya domin samun damar watsa jawabin kai tsaye.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu domin bikin tunawa da ranar samun ƴan cin kan.

More from this stream

Recomended