Shugaban ƙasa,Bola Ahmad Tinubu zai bar birnin Abuja a ranar Laraba ya zuwa birnin Faris inda zai yi wata ziyarar aiki ta kwanaki uku.
A wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, Bayo Onanuga mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan sadarwa da tsare-tsare ya ce Tinubu zai kai ziyarar ne bisa gayyatar da shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron ya yi masa.
Onanuga ya ce ziyarar za ta mai da hankali wajen bunƙasa alaƙa ta bangaren siyasa, tattalin arziki, al’adu da kuma samar da karin damarmaki dake buƙatar haɗin gwiwa musamman a bangaren noma tsaro, ilimi, ayyukan yi da kuma kiwon lafiya.
Ya ƙara da cewa dukkanin shugabannin biyu za su halarci taro a tsakanin ƴan kasuwar Faransa da na Najeriya.