Tinubu ya ziyarci Obasanjo

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC,Bola Ahmad Tinubu ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a gidansa dake Abeokuta babban birnin jihar Ogun.

Babu wani bayani kan dalilin ganawar ta su sai dai masu sharhi na ganin hakan baya rasa nasaba da takarar shugaban kasa da Tinubu yake yi.

A yayin ziyarar Tinubu na tare da gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da kuma Ooni na Ife, Adeyeye Enitan.

A baya dai Tinubu da Obasanjo basa ga muci da juna tun bayan saɓanin da suka samu lokacin yana gwamnan Lagos shi kuma Obasanjo yana shugaban kasa.

More from this stream

Recomended