Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da sunan Dr. Bernard Mohammed Doro zuwa Majalisar Dattawa domin tabbatar da shi a matsayin sabon minista daga Jihar Filato.
Wannan na zuwa ne bayan nadin tsohon Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, a matsayin Shugaban na Jam’iyyar APC ta ƙasa baki ɗaya.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, inda ya ce nadin ya dogara ne da amincewar Majalisar Dattawa.
Onanuga ya ce an riga an tura cikakken bayanin sabon wanda aka zaɓa zuwa majalisar domin tantancewa.
An haifi Dr. Bernard Doro a ranar 23 ga Janairu, 1969, a ƙauyen Kwall dake cikin Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Filato.
A cewar Onanuga, Doro na da fiye da shekaru 20 na ƙwarewa a fannoni daban-daban, ciki har da aikin likitanci, kula da magunguna, jagoranci mai ma’ana, da hulɗar al’umma a ƙasashen Birtaniya da Najeriya.
Nadin Doro ya zo ne a wani lokaci da ake ci gaba da sake tsara shugabancin gwamnati domin tabbatar da ingantaccen aiki da wakilcin jihohi a majalisar ministoci.
Tinubu Ya Zaɓi Bernard Doro a Matsayin Minista Daga Jihar Filato
