Tinubu ya yabawa jami’an tsaro kan sakin ɗaliban makarantar sakandaren Maga

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi marhabin lale da sakin dalibai 24 na Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Maga dake karamar hukumar Danko Wasagu da wasu yan bindiga suka sace a ranar 17 ga watan Nuwamba.

A ranar Talata ne aka sako ɗaliban bayan da suka shafe kwanaki a hannun yan bindigar

Da tsakar dare ne aka sace ɗaliban a ranar da wata tawagar jami’an soja dake harabar makarantar suka janye da wurin.

A wata sanarwa ranar Talata Tinubu ya yabawa jami’an tsaro kan kokarin da su ka yi da ya kai ga sakin ɗaliban.

Ya shawarci jami’an tsaro da su kara matsa kaimi wajen ganin an ceto sauran ɗalibai dake tsare a hannun yan bindiga.

“Naji dadi da aka samu dukkanin daliban mata 24,” a cewar Tinubu kamar yadda mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya jiwo ya na faɗa.

More from this stream

Recomended