Tinubu Ya Umarci Matawalle Ya Koma Jihar Kebbi Kan Sace Dalibai Mata 25

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Ministan Ƙananan Harkokin Tsaro, Bello Matawalle, da ya tashi cikin gaggawa zuwa Jihar Kebbi domin bin diddigin matsalar sace dalibai mata 25 da ’yan bindiga suka yi a jihar.

A wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan bayanai da dabarun yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, an ce Matawalle zai zauna a jihar har sai an kammala aikin haɗin-gwiwar jami’an tsaro don ceto ɗaliban.

Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindiga sun kai farmaki a wayewar gari a ranar Litinin inda suka yi awon gaba da dalibai 24 daga Government Girls Comprehensive Secondary School da ke Maga, a Jihar Kebbi.

Matawalle, wanda ya taɓa zama gwamnan Zamfara daga 2019 zuwa 2023, ya samu gogewa wajen fuskantar barazanar ’yan bindiga da garkuwa da mutane, ciki har da sace dalibai mata 279 a Jangebe a shekarar 2021, kafin daga baya a sako su.

Sanarwar ta ƙara da cewa Tinubu ya dage ziyararsa zuwa Johannesburg da Luanda saboda jiran ƙarin bayanai kan lamarin sace ɗalibai a Kebbi da kuma harin da aka kai wa mabiya cocin Christ Apostolic a Eruku, Jihar Kwara.

More from this stream

Recomended