Firaiministan Burtaniya Keir Starmer a yammacin Laraba ya tattauna da shugaban Najeriya Bola Tinubu ta wayar tarho.
Shugaban kasar ya taya firaministan murnar lashe zaben da ya gudana a baya-bayan nan, sannan kuma firaministan ya yaba wa shugaban kasar a daidai lokacin da Najeriya ke cika shekaru 25 na mulkin dimokradiyya ba tare da yankewa ba, kamar yadda wata sanarwa da aka wallafa a shafin intanet na gwamnatin Burtaniya ta ce.
A cewar sanarwar, firaministan ya yi tsokaci kan muhimmiyar alakar da ke tsakanin Birtaniya da Najeriya, ta hanyar yin hadin gwiwa kan harkokin kasuwanci da tsaro a matsayin kawancen kasashen Commonwealth, tare da dadaddiyar alakar da ke tsakanin mutanen biyu.
“Shugabannin sun yi maraba da wannan lokaci a matsayin wata dama ta sake farfado da wannan dangantaka, tare da yin aiki kafada da kafada don bunkasa tattalin arziki da wadata a tsakanin kasashenmu, ciki har da inganta hadin gwiwar cinikayya da zuba jari,” in ji shi.