Tinubu ya tafi ƙasar China

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya tashi daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja akan hanyarsa ta zuwa ƙasar China.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis ya ce shugaban ƙasar zai yada zango a ƙasar Haɗaɗdiyar Daular Larabawa akan hanyar ta sa.

” A ƙasar China shugaban ƙasar zai gana da shugaba Xi Jinping kuma zai gudanar da taro da ƴan kasuwar ƙasar ta China a wurin taron ƙasashen Afrika da China,” a cewar sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa Tinubu zai samu rakiyar wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati.

Ziyarar ta Tinubu na zuwa ne ƴan kwanaki kaɗan bayan ziyarar da ya kai ƙasar Faransa.

More News

Jam’iyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Jam'iyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Dino Melaye tsohon ɗantakarar gwamna a jihar kan zargin cin amanar jam'iya. Shugabannin jam'iyar PDP na mazaɓar...

Sojoji sun kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Buzu

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kashe gawurtaccen ɗan bindiga Kachalla Halilu Sububu wanda aka fi sani da Kachalla Buzu. An kashe Kachalla ne...

Dakarun Najeriya sun hallaka ƴanbindiga a Neja

Rundunar sojin saman Najeriya ta hakala 'yanbindiga sama da 28 a yankin ƙaramar hukumar Shiroro dake jihar Neja.Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai...

Tinubu ya gana da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya a fadar Buckingham a wata ziyara da yakai. Wannan ce ganawa...