Tinubu ya sanya hannu kan dokar mafi ƙarancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan sabuwar dokar gyara mafi karancin albashi na kasa na 2024 ta zama doka.

Dokar dai za a sake duba ta duk shekara uku.

Hakan ya biyo bayan kudurin da gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin kwadago suka yi na biyan mafi karancin albashi na N70,000.

Tinubu ya sanya hannu ne a fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Litinin bayan da majalisar dokokin kasar ta amince da kudirin.

Shugaban ya rattaba hannu kan kudirin dokar a tsakiyar zaman majalisar zartarwa ta tarayya.

Shugaban ma’aikatan gwamnati ya ce babu shakka sabuwar dokar za ta tabbatar wa ma’aikata cewa shugaban ya damu da jin dadin su.

More from this stream

Recomended