Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya rantsar da mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin mai riƙon muƙamin Babbar Mai Shari’a ta Najeriya.
Bikin rantsuwar ya gudana ne ranar Juma’a a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock dake Abuja.
Rantsarwar da aka yi ma Kekere-Ekun yasa ta zamo mace ta biyu da ta taɓa zama Babbar Mai Sharia ta Najeriya bayan Maryam Alooma Muktar wacce ta rike muƙamin daga shekarar 2012 zuwa 2014.
Mai riƙon muƙamin Babbar Mai Shari’a ta Najeriya ta karɓi rantsuwar kama aiki da misalin ƙarfe 11:38 kana ta samu wuri ta zauna a kujerar da aka ware mata a zauren wurin taron.
A cikin waɗanda suka halarci bikin akwai shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu da shugabancin majalisar wakilai.